Lauyan da ke kare Muhammad Mahdi Akef tsohon shugaban kungiyar Ihwanul-Muslimin ta Muslim Brootherhood ta kasar Masar ya bayyana cewa: Jami'an tsaron Masar a jiya Juma'a sun sanar da shi cewa ya sanar da iyalan Muhammad Mahdi Akef cewa dan uwansu ya rasu a jiya Juma'a bayan fama da rashin lafiya a gidan kurkuku.
Mahukuntan kasar Masar suna tsare da Muhammad Mahdi Akef ne a gidan kurkuku tun bayan kifar da gwamnatin Muhammad Morsi na kungiyar Ihwan a shekara ta 2013 kan zargin hannu a dauki ba dadin da aka yi tsakanin 'yan kungiyar Ihwan da masu adawa da gwamnatin Morsi, sannan wata kotu a kasar ta zartar da hukuncin daurin shekaru 25 kansa a gidan kurkuku.
Marigayi Muhammad Mahdi Akef ya karbi ragamar shugabancin kungiyar Ihwan ne a shekara ta 2004 bayan rasuwar shugabanta Muhammad Ma'amun Al-hudhiybi, sannan ya mika ragamar shugabancin ga Mahammad Badi'e a shekara ta 2010, kuma Allah ya yi masa rasuwa ne a jiya Juma'a 22 ga watan Satumban shekara ta 2017 yana da shekaru 89 a duniya.288